
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa mutane 8 ne su ka rasa rayukansu, sannan 26 su ji raunuka a harin da ƴan ta’adda su ka kai wa jirgin ƙasa ƙirar AK9 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar ta ce, hukumomin tsaro mlne su ka bada ƙididdigar ga gwamnatin Kaduna.
Ya ce Gwamnatin Kaduna ta samu cikakken kundin sunayen fasinjojin da ke kan jirgin da ga wajen Hukumar kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Ƙasa, NRC.
Ya ce a kundin da gwamnatin ta samu, an nuna cewa fasinjoji 398 ne su ka sayi tikiti, amma 362 a ka tantance su kannau jirgin, inda ya ƙara da cewa kundin sunayen fasinjojin bai haɗa da na ma’aikatan jirgin da jami’an tsaron jirgin ba.
Ya ce a na ci gaba da bincike domin gano sauran fasinjojin da su ka hau jirgin amma ba a samu bayanan su ba.