Home Labarai Mutane 2 sun mutu, 6 sun maƙale bayan da gini mai hawa bakwai ya ruguje a Legas

Mutane 2 sun mutu, 6 sun maƙale bayan da gini mai hawa bakwai ya ruguje a Legas

0
Mutane 2 sun mutu, 6 sun maƙale bayan da gini mai hawa bakwai ya ruguje a Legas

Wani gini mai hawa bakwai da ba a kammala ba ya ruguje a titin Oba Idowu Oniru da ke unguwar Lekki a jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa a ƙalla mutane shida aka ce sun maƙale a cikin ɓaraguzan ginin da ya ruguje – kuma an ce mutane biyu sun mutu.

An tura masu ba da agajin gaggawa don fara aikin ceto.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Olufemi Oke-Osanyintolu, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), ya ce hukumar ta bazama domin ɗaukar matakin.

“Bayan isa wurin da lamarin ya faru, sai aka ga wani gini mai hawa 7 da ba a kammala shi ba ya ruguje,” in ji Oke-Osanyintolu.

“An ba da rahoton mutane shida sun makale a karkashin baraguzan ginin da ya ruguje wa

“Za a bukaci na’urar tona kayan aiki masu nauyi na hukumar domin ceto wadanda suka makale. Mun kunna tsarin mayar da martani na jihar Legas.”