
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, reshen Jihar Filato ta ce mutane 10 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 15 suka samu raunuka a wani haɗarin mota da ya rutsa da su a kan babbar hanyar Jos zuwa Bauchi.
Kwamandan sashen, Alphonsus Godwin ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a Jos, inda ya ce, haɗarin ya haɗa da wata babbar mota tare da ƙananan motoci guda shida.
A cewar Godwin, wani yaron direban babbar motar dakon kaya ne kan motar ya ƙwace masa, ya kuma rasa yadda zai shawo kanta lokacin da ta samu matsala.
“Motar ta hau kan motoci da dama, lamarin da ya haddasa haɗurra da dama a kan babbar hanyar, inda mutane goma su ka rasa rayukansu a nan take, yayin da wasu goma sha biyar suka samu munanan raunuka.
“Wadanda suka samu raunuka an kwantar da su a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Toro, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham, Jos.
Godwin ya shawarci masu manyan motoci da su tabbatar da kula da ababen hawansu yadda ya kamata, da sanya idanu kan direbobin su da kuma daina baiwa yaran da shekarunsu bai kai ba tuƙi.