
Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane biyar da tarin yashi ta danne su a kauyen Yanlami da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a jihar.
A sanarwar da kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ya fitar, hukumar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da safe.
A cewar Abdullahi, shelkwatar hukumar ta karbi rahoto na gaggawa da ga ofishin ta na Bichi cewa yashi ya rufto wa mutane su biyar, inda ya ƙara da cewa ba a yi wata-wata ba a ka aika da jami’ai domin yin ceto da misalin 11:05 na safe.
Abdullahi ya bada sunayen mamatan da su ka haɗa da Alasan Abdulhamid, mai shekara 22, Jafaru Abdulwahabu, shekara 30, Jibrin Musa, shekara 30, Masaudu Nasiru, shekara 25 sai kuma Muhammad Sulaiman, mai shekara 35.
Kakakin ya yi bayanin cewa mamatan sun gamu da ajalinsu ne bayan da su ke ɗiban yashin a wani kudiddifi domin su taya abokinsu gina gidansa sakamakon aurensa ya gabato.
“Su na cikin aikin ne sai kawai yashin ya rufto a kan su inda su ka rasu,” in ji Abdullahi.
Ya ce an danƙawa ƴan sanda da dagacin kauyen Yanlami gawawwakin mamatan.