
Solomon Dalung, tsohon Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, ya ce al’ummar Nijeriya, a zaben 2023 ingancin ƴan takara za su zaɓa ba jam’iyyunsu ba.
Dalung, wanda shi ne dan takarar Majalisar Wakilai a mazabar tarayya ta Langtang North/Langtang ta Kudu, a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, ya bayyana haka ne a yau Talata a Jos, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.
Tsohon minista6 ta ce ƴan Nijeriya sun fi sanin harkokin siyasa, kuma abin da suke yi a fagen siyasar yanzu ya nuna sun fi damuwa da halayen ƴan takara ne ba jam’iyyunsu ba.
“Kada a yaudare ku, ‘yan Najeriya ba za su zabi jam’iyyu ba, ‘yan Najeriya za su zabi daidaikun mutane ne.
“Zai zama gamayyar bakan gizo a 2023, kuma gamayyar bakan gizo ce ta ceci Afirka ta Kudu saboda kawo karshen mulkin wariyar launin fata.
“A shekarar 2023 ‘yan Najeriya da kuri’unsu za su gina kawancen bakan gizo wanda zai kawo karshen wannan gazawar a siyasa da yan bangar siyasa da kafa harsashin sabuwar kasa.
“Al’ummar da mutane daga bangarori daban-daban na siyasa, akidu daban-daban, addinai daban-daban, kabilu daban-daban za su hadu, su gina kasa mai inganci ga Nijeriya,” in ji shi.
Tsohon ministan ya ce ayyukan ci gaba na wanda aka zaba shi ne makamin da zai iya amfani da shi don tsira a zaben 2023.