
Wani dan kasar Iran da ake yi wa lakabi da “mutum mafi dauɗa a duniya” saboda rashin yin wanka tsawon shekaru ya rasu yana da shekaru 94, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na kasar su ka ruwaito a yau Talata.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya rawaito cewa, Amou Haji, wanda ya kwashe sama da rabin ƙarni bai yi wanka ba kuma bai yi aure ba, ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata a kauyen Dejgah da ke lardin Fars da ke kudancin kasar.
Haji ya guje wa yin zuba ruwa a jikinsa sabo da fargabar “kamuwa da rashin lafiya”, IRNA ya ruwaito wani jami’in yankin ya na cewa.
Amma “a karon farko a ƴan watannin da suka gabata, mutanen kauyen sun kai shi bandaki don yi masa wanka,” in ji IRNA.
An yi wani ɗan gajeren fim ɗin shi mai taken “The Strange Life of Amou Haji” game da rayuwarsa a shekarar 2013, kamar yadda kafafen yada labaran Iran suka bayyana.