
Wani sabon mutum-mutumin fitaccen ɗan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo ya haifar da bore a Jihar Goa da ke Indiya.
Al’ummar jihar Goa ɗin sun soki yadda a ka karrama Ronaldo a maimakon wani ɗan wasan ƙasar.
Michael Lobo, Minista a Jihar ta Goa, ya ce an gina mutum-mutumin ne domin bunƙasa wasan ƙwallon ƙafa da kuma ƙarfafa gwiwar matasa a kan wasan.
Sai ga shi a ranar da za a ƙaddamar da gunkin, mai nauyin kilogiram 400, sai mutane su ka fara bore, inda su ka yiwa wajen tsinke riƙe da baƙaƙen tutoci, kamar yadda wata jaridar indiya mai suna IANS ta rawaito a yau Laraba.
Ba ma kuma wai gunkin Ronaldo kaɗai jama’a ke nuna goyon baya ba, har da ma zaɓo ɗan wasa da ga Portugal, duk da cewa ƙasar ta raini jihar ta Goa tsawon shekaru da dama har sai bayan shekaru 60 sannan ta bar jihar.