
Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar, ɗan shekara 38 bisa ƙona wani masallaci da masallata ke tsaka da sallar asuba.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Gadan da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a yau Laraba da asuba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta cafke matashin da ake zargi da cinna wa masallacin wuta a lokacin da mutane fiye da 30 ke sallar Asuba a ciki.
A wata sanarwar da rundunar ta fitar, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin mai suna Shafi’u Abubakar mai shekara 38 ya yi sanadiyyar ƙonewar mutane.
Tuni dai aka kwashe mutum 24 waɗanda suka ƙone zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu.
SP Kiyawa ya ƙara da cewa binciken da aka gudanar dai ya nuna cewa an yi amfani da man fetir ne wajen cinna wutar.
Dangane kuma da dalilin faruwar al’amarin, SP Kiyawa ya ce “matashin ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon ƙin raba gado a tsakanin danganinsa, inda ya ce waɗanda suka zalunce shi ɗin suna cikin masallacin a lokacin da suke sallah. Kuma ya yi hakan ne domin ya aike da saƙo.” In ji matashin.
A nashi ɓangaren, Shugaban rundunar ƴansanda Shiyyar ta ɗaya a Kano, AIG Umar Sanda ya tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, yayin da sauran 23 ke karbar magani a asibitin.
Ya baiyana hakane lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad a Kano.
Ya ce lamarin, wanda aka yi amfani da abun fashewa kirar gida, bashi da alaka da aikin ta’addanci, inda ya ce rigimar gado ce ta haddasa lamarin.