
Daga Hassan Y.A. Malik
Rundunar ‘Yan sandan jihar Kwara ta bayyana cafke kasurgumin barawon da ake zargi da jagorantar harin da aka kai bankuna shida a garin Offa a jihar Kwara wanda ya yi sanadiyyar rayukan ‘yan sandan 9 da wasu mutane 8.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ACP Jimoh Moshood ya bayyana neman wannan jagoran da wasu guda uku a makon da gabata ya ruwa a jallo wanda ake zargin da hannu dumu dumu a mumunan harin garin Offa.
An yi nasarar cafke Micheal Adikwu wanda tsohon jami’in dan sanda ne na rundunar yaki da masu fashi da makami inda aka tube masa rigar ‘yan sanda a shekarar 2012.
An kori Adikwu daga aikin ‘yan sanda bayan ya taimakawa wasu barayin da aka kama tserewa daga komar ‘yan sanda inda ya share shekaru uku a gidan yari, daga baya ya kafa kungiyar fashi da ta addabi al’ummar jihar Kwara bayan ya fito daga gidan yari.
A yanzu haka dai, Adikwu yana tsare a wajen ‘yan sanda kuma gwamnatin jihar Kwara ta yi alkawarin bada naira miliyan 5 ga duk wanda ya fallasa maboyar sauran barayin da ake nema ruwa a jallo.
Haka zalika, rundunar ‘yan sandan sun bayyana cafke wasu mutane guda 20 wadanda ake zargi da hannu a harin.