
Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC da ke yankin Legas sun cafke wani mutum mai suna Precious Ofure Omonkhoa a bisa zargin damfarar al’umma ta harkar cinikaiyar sulalla ta yanar gizo, wacce a ka fi sani da bitcoin.
Dubun Omonkohoa ta cika ne inda a ka cafke shi a yankin Ikoyi da ke Jihar Legas a ranar 8 ga watan Nuwamba ba da hukumar ta samu cikakken bayanan sirri a kansa.
Hukumar na zargin Omonkohoa da yin basaja a zuwan shi bature ne ɗan ƙasar Sweden mai suna Moshem Cnich, inda ya riƙa damfarar bayin Allah ta yanar gizo a zuwan wai shi mai yin harkar bitcoin ne har sai da ya tara $200,000.
Bincike ya bayyana cewa tuni ɗan damfarar ya sayi fili na kimanin $150,000 ta hanyar bitcoin ɗin, sannan bayan da a ka cafke shi, an samu $50,000 a asusun ajiye sulalla na bitcoin, wanda a ka fi sani da wallet.