Home Labarai Na sha alwashin ganin bayan Ganduje a zaben 2019 – Kwankwaso

Na sha alwashin ganin bayan Ganduje a zaben 2019 – Kwankwaso

0
Na sha alwashin ganin bayan Ganduje a zaben 2019 – Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

 

Hassan Y.A. Malik

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alwashin sai ya tunkude gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje daga kujerar gwamna a kakar zaben 2019.

Kwankwaso dai ya bayyana hakan ne a gidansa na Kaduna, a lokacin da wata tawaga daga karamar hukumar Warawa ta kai masa ziyarar ban girma da nuna goyon baya a karshen makon da ya gabata.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai wani gidan rediyo mai zaman kansa a jihar Kano mai suna Express Radio FM ya sanya muryar Kwankwason yana gabatar da wancan zance na kwabe magajinsa, tsohon mataimakinsa a zabe mai zuwa.

An jiyo Kwankwaso na fada cikin murya da ke nuna hasala cewa babu wata kama karya ko karfafa da za su  hana ya doka Ganduje da kasa a zaben 2019.

A ta bakin Sanata Kwankwaso, “In na yi nasarar cire Ganduje a shekarar 2019, zan tabbata har masu goya masa baya masu sanya da khaki su ma an yi waje da su (yana magana ne akan kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano).”

Kwankwaso ya koka kan yadda Ganduje ya ki ci gaba da ayyukan alheri da ya kafa kamarsu tallafin karatu zuwa kasashen waje, ciyar da dalibai ‘yan firamare da dai sauran aikace-aikace.

Kwankwaso ya bayyana bakin cikinsa kan yadda gwamnati ta hana shi shiga Kano don ya gana da Kwankwasawa a ranar 30 ga watan Janairu.

Daga karshe dai Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da su bashi hadin kai wajen ganin ya cimma bukatarsa ta dankara Ganduje a kasa a zaben 2019.

Gidan Kwankwaso na Kaduna dai a halin yanzu ya zama farfajiyar gudanar da harkokin siyasar a, inda daruruwan magoya baya kan kai masa caffa a karshen kowane mako.