Home Labarai NACA ta tallafawa masu cutar sida 75 a Kano

NACA ta tallafawa masu cutar sida 75 a Kano

0
NACA ta tallafawa masu cutar sida 75 a Kano

Hukumar Kula da Cutar Sida, NACA ta tallafawa masu ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, wacce a ka fi sani da HIV, a kan sana’o’i guda uku.

Darakta-Janar na hukumar, Dakta Aliyu Gambo ne ya faɗi hakan yayin da ya ke raba takardar shaidar kammala horo ga  waɗanda su ka amfana da shirin.
Gambo, wanda ya samu wakilcin ma’aikaciya a hukumar, Hafsah Gumel, ya ce an koyawa masu ɗauke da cutar gashe-gashen kayan fulawa, kwalliya da kuma gyaran gashi.
Ya ƙara da cewa tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen rage yaɗuwar cutar.
Darakta-Janar ɗin ya kuma baiyana cewa kowanne mutum da ya amfana da horon za a bashi naira dubu 75 a matsayin jari.
Ya ƙara da cewa bayan mata 75 za a baiwa takardar shaida, akwai maza su ka da za su amfana da tsarin.
Tun da fari, waɗanda su ka shirya shirin sun yi kira ga waɗanda su ka amfana da su tabbatar sun yi amfani da kuɗin nan yadda ya dace.
Amina Isa, wacce ta wakilci waɗanda su ka amfana, ta godewa NACA da sauran abokan hulɗar ta da su ƙaddamar da shirin.