
Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Ƙasa Hidima ta Kasa, NYSC, ta sanar da ƙarin matsayin Daraktar Watsa Labarai da Fasahar Sadarwa, Christy Uba a matsayin Darakta-Janar ta riko a hukumar.
Ta yiwu Uba ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da aka nada shugabar hukumar NYSC tun bayan kafa ta kimanin shekaru 50 da su ka gabata.
Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulda da Jama’a na NYSC, Eddy Megwa ya fitar a jiya Talata, ta ce nadin ya biyo bayan korar Birgediya Janar, Muhammad Kaku Fadah a matsayin shugaban hukumar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.
Sanarwar mai taken, ‘Mrs Uba za ta riƙe ragamar NYSC har sai an naɗa babban Darakta Janar na dindindin.
“Darakta mafi girma ta karbi jagorancin kungiyar a matsayin mai kulawa, har zuwa lokacin da Shugaban kasa ya nada babban Darakta na dindindin”, in ji Megwa.