
Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya ce bai yi nadamar sauya sheƙa zuwa jam’iyar APC ba.
Umahi ya baiyana haka a yau Laraba yayin da ya ke jawabi ga ƴan jam’iya da magoya bayan sa a wani gangamin nuna goyon baya a Abakaliki.
Umahi, wanda ya yi kira da a kwantar da hankula ya tabbatar wa da ƴan jam’iya da masoyansa da su ka halarci gangamin da cewa hukuncin kotun danya cire shi a matsayin gwamna ba tabbatacce ba ne.
Ya kuma nanata cewa bai yi nadamar barin PDP ba , wacce ya ce ba a bin da ta sa a gaba sai ci wa gwamnatinsa dunduniya.
Ya tabbatar da cewa hukuncin kotun ba zai wuce ba a kotun koli, inda ya jaddada cewa shi ne gwamna har yanzu kuma yana nan ya na aikin sa a matsayin gwamna.