
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta sanar da janye duk wani sabulun wanka na Dove mai lamba 81832M 08 daga kasuwannin Nijeriya.
An bada sanarwar janye sabulu, wanda ake yin sa a kasar Jamus saboda gano wani gurbataccen sinadari mai cutarwa.
A cewar NAFDAC, sabulun ya saba wa ka’idar kasuwancin kayan kwalliya ta kasa, BMHCA, saboda an gano ga na dauke da sinadarin Butylphenyl Methylpropional, wanda aka fi sani da Lilial.
Wannan sinadari yana da alaƙa da haɗarin lafiya mai tsanani, gami da cutarwar haihuwa da yuwuwar illa ga jariran da ba a kai ga haifar su ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, NAFDAC ta yi karin bayani kan illar da ke tattare da BMHCA, inda ta yi nuni da cewa, an haramta su ne a cikin kayan kwalliyar saboda yuwuwar ta na haifar da matsalolin haihuwa da kuma illa ga fata, wanda ke haifar da rashin lafiyar masu amfani da su.
“Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) tana fadakar da jama’a game da janye Sabulun wanka na Dove Beauty Cream Bar (100g) mai lamba 81832M 08, wanda ake yin sa a kasar Jamus, saboda gurbatar sinadarai.