Home Labarai NAHCON ta bada haƙuri kan barin maniyyata 1,551 ba su je aikin Hajji ba

NAHCON ta bada haƙuri kan barin maniyyata 1,551 ba su je aikin Hajji ba

0
NAHCON ta bada haƙuri kan barin maniyyata 1,551 ba su je aikin Hajji ba

 

 

 

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta bada haƙuri kan gaza kwashe dukka maniyyatan ƙasar nan zuwa Saudi Arebiya domin aikin Hajjin bana.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa maniyyata 1,551 ne, daga jihohi 3 da kuma na kamfanonin sufuri basu samu zuwa aikin Hajjin bana ba.

A wata sanrwa da NAHCON ɗin ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami’ar hulɗa da jama’a, Fatima Sanda Usara, hukumar ta ce maniyyata 9 daga jihar Bauchi; 91 daga jihar Filato; 700 daga jihar Kano da kuma kimanin 750 daga ɓangaren kamfanonin sufuri ne basu samu zuwa aikin Hajji ba.

A sanarwar, NAHCON ta nuna takaicin faruwar lamarin, inda ta baiwa waɗanda abin ya shafa hakuri.

Hukumar ta kuma yi alkawarin maida wa kowa kuɗaɗen Hajji da ya biya, inda ta bayyana cewa ta ɗauki darussa masu yawa a kan matsalar da a ka samu, ta kuma ci alwashin gyara wa a shekaru masu zuwa.

“Abin takaicin shi ne, duk da kokarin da aka yi na jigilar dukkan maniyyatan Najeriya da ke son zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2022, NAHCON ta gaza wajen sauke wannan nauyi, musamman sakamakon koma bayan da aka samu a karshen makon da ya gabata da ya kawo cikas ga shirinta na kammala jigilar maniyyatan zuwa ranar 27 ga watan Yuni na wannan shekara.

“Sai dai abin takaicin shi ne, zabin jirage da aka yi hayar da ya baiwa hukumar NAHCON da kuma masu gudanar da jigilar maniyyatan kamfanonin yawon bude ido masu zaman kansu su ma ya ci tura saboda asusunsu na IBAN ya gaza samun amincewar hukumomin Saudiyya.

“Musamman, wadannan adadin maniyyatan da abin ya shafa ba za su je Saudiyya kafin rufe filin jirgin sama na Jeddah ba, don haka za su yi hajjin bana. Su ne: Mahajjata tara (9) daga jihar Bauchi; Alhazai 91 daga jihar Filato; Mahajjata 700 ne daga jihar Kano da kuma mahajjata kimanin 750 daga bangaren masu yawon bude ido masu zaman kansu,”