Home Ilimi Naira biliyan 2 mu ke buƙata domin shirya jarrabawa mai zuwa — NECO

Naira biliyan 2 mu ke buƙata domin shirya jarrabawa mai zuwa — NECO

0
Naira biliyan 2 mu ke buƙata domin shirya jarrabawa mai zuwa — NECO

 

Hukumar shirya Jarrabawar Fita da ga Makarantun Sakandare ta Ƙasa,. NECO, ta baiyana cewa Naira Biliyan 2 ta ke buƙata domin shirya jarrabawa mai zuwa.

Shugaban hukumar na ƙasa, Ibrahim Dantani ne ya baiyana hakan a yayin buɗe wani taron ƙara wa juna sani a kan tabbatar da ingancin ilimi, wanda ya gudana a Minna, Jihar Naija.

Dantani ya ce hukumar na bukatar adadin kuɗin ne domin biyan ma’aikatan ta 4,000 da su ke aikin gudanar da jarrabawar a faɗin ƙasar nan.

Ya alaƙanta kuɗaɗen shirya jarrabawa da ƙarin ƙudaden tafiye-tafiye na hukumar NECO ɗin daga N16,000 zuwa N33,500.

Shugabann ya baiyana cewa NECO ba ta da kuɗin da za ta aiwatar da wannan tsarin ƙarin ƙudaden tafiye-tafiye, inda ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta kawo wa hukumar ɗauki.

Ya kuma yabawa gwamnati a bisa yunkurin da ta ke yi na daina karɓar kashi 25 cikin ɗari na kuɗaɗen jarrabawa da ga hannun NECO.