Home Kasuwanci Darajar Naira ta sake faɗuwa a kan Dalar Amurka

Darajar Naira ta sake faɗuwa a kan Dalar Amurka

0
Darajar Naira ta sake faɗuwa a kan Dalar Amurka

 

 

Naira ta yi faɗuwar wanwar a kan Dala a jiya Laraba a kasuwar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki, inda aka yi musanya a kan N426.58.

Adadin ya nuna faduwar darajar Nairar da kashi 0.57 idan aka kwatanta da N424.17 da aka yi hada-hada da Dala a ranar Talata.

Hada-hadar ta rufe ne a kan bayyanannen farashi na N426.50 a Dala a jiya Laraba.

Canjin N444 zuwa Dala shi ne mafi girman farashin da aka samu a cinikin yau kafin ya daidaita a kan N426.58.

Ana siyar da Naira a kan N414 ga Dala a kasuwar ranar.

An yi cinikin Dala miliyan 144.03 a musayar kuɗaɗen waje a kasuwar masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki a jiya Laraba.