Home Labarai Naja’atu Muhammad ta fallasa badaƙalar kuɗaɗe a Hukumar kula da Harkokin Ƴan Sanda, PSC

Naja’atu Muhammad ta fallasa badaƙalar kuɗaɗe a Hukumar kula da Harkokin Ƴan Sanda, PSC

0
Naja’atu Muhammad ta fallasa badaƙalar kuɗaɗe a Hukumar kula da Harkokin Ƴan Sanda, PSC

 

 

 

Kwamishiniya a Hukumar kula da Harkokin Ƴan sanda ta Ƙasa, PSC, Naja’atu Muhammad, ta kai ƙorafi zuwa Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin kasa Zagon-ƙasa, EFCC, inda ta yi ƙorafin badaƙalar kwangilar miliyoyin naira, da almubazzaranci da kuɗaɗe da kuma rashin bin ka’ida wajen tafiyar da harkokin hukumar.

A cikin takardar ƙorafin, mai ɗauke da kwanan watan 29 ga watan Yuni, 2022, Muhammad, wacce ke wakiltar Arewa-maso-Yamma a hukumar, ta yi zargin cewa shugaban hukumar, Musiliu Smith, ya bayar da kwangiloli na bogi ba tare da bin ka’ida ba.

Kwamishiniyar ta lura cewa kwamitin gudanarwa, wanda ke da alhakin amincewa da kashe kuɗaɗe, musamman ma na yin manyan ayyuka, sau biyu kawai kwamitin ya taɓa zama domin gana wa tun bayan ƙaddamar da shi a shekarar 2018.

“Kwamitin Gudanarwa yana kama da Majalisar Zartarwa ta Tarayya, inda aka amince da kashe kudaden gwamnati. Sashi na 12, 13 da 14 na hukumar ya tanadi kuɗaɗen da kashe kuɗaɗen hukumar.

“amma kuma, tun da muka shigo a matsayin kwamishinoni, shekaru 4 da suka wuce, sau biyu kawai aka yi taron gudanarwa.

Ta kara da cewa “Shugaban Hukumar ba shi da wani iko da hannu ɗaya ya amince da duk wani kashe kudi da kuma a madadin hukumar sai dai kamar yadda hukumar gudanarwar danya ke shugabanta ya amince da ita.”

Wani ɓangare na korafin ya ce: “A ranar 11 ga Mayu, 2022, ba tare da amincewar kwamitin gudanarwa ba, shugaban ya bayar da kwangilar ko kuma ya sa a ba shi kwangilar kuma ya biya N34,749,375 a matsayin kashi 50 na kudin da aka biya ga kamfanin na EMPLUG LTD domin tsarawa da ƙirƙirar manhajar ɗaukar aikin ɗan sanda ta yanar gizo a hukumar.

“amma sai a yi amfani da takardu na boge, kamar su takardar rubutaccen bayanan da a ka tattauna a yayin gana wa da sauransu, da su ke nuni da an amince wajen amincewa da kwangilolin, gaskiyar ita ce babu wani izinin gudanarwa na wannan kwangilolin,” in ji ta.