Home Cinikayya Najeriya da Swizalan sun cimma yarjejeniyar dawo da dala miliyan 321 daga cikin kudin da Abacha ya kwasa

Najeriya da Swizalan sun cimma yarjejeniyar dawo da dala miliyan 321 daga cikin kudin da Abacha ya kwasa

0
Najeriya da Swizalan sun cimma yarjejeniyar dawo da dala miliyan 321 daga cikin kudin da Abacha ya kwasa
Tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Janar Sani Abacha

Babban Antini Janar na Najeriya kuma ministan Shari’ah Abubakar Malami SAN, ne ya tabbatar da cewar, tuni Gwamnatin Najeriya da takwararta ta Swizalan suka gama cimma yarjejeniyar dawowa da najeriya kudi kimanin dalar Amurka miliyan 321, daga cikin dumbin kudaden da tsohon shugaban kasa Gen. Sani Abacha ya kwasa daga baitulmalin Najeriya ya kai kasar ya jibge.

Mai magana da yawun Ministan Salihu Isa, shi ne ya sanar da cewar ministan Abubakar Malami ya bayyana hakan a wajen wani taron karawa juna sani kan dabarun dawo da kudaden sata. Kudin dai wani bangare ne na kudadenrijiyar Mai ta Malabu da ke ta taƙaddama akanta.

Malami ya kara da cewar, nan gaba a watan Disamba ne ake sa ran kammala sanya hannu akan takardun yarjejeniyar dawowa da najeriya kudaden a birnin Washinton DC na ƙasar Amurka.

Ko me zaku ce game da badaƙalar rijiyar Malabu da ta sake kunno kai?