
Wasu ƴan Nijeriya mazauna kasashen waje sun bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da zaɓen 2023
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) na cikin wadanda ake kara a karar da su ka shigar na neman a bi musu hakkinsu na kaɗa kuri’a a zaben kasar.
Wadanda su ka shigar da karar sun haɗa da Chikwe Nkemnacho, Barista, da Kenneth Azubuike Nkemnacho, wadanda dukkansu mazauna kasar Ingila ne (Birtaniya).
A cewarsu, sun shigar da karar ne a madadin sauran ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, na duniya.
A karar mai lamba FHC/ ABJ/ CS/2119/2022 da lauyansu Augustine Temfeh-Nkemnacho ya shigar, masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta dakatar da shugaban kasa da INEC daga ci gaba da gudanar da shirye-shirye na zaben 2023.
Sun kuma nemi da a sabunta rajistar masu zabe na INEC mai ɗauke da cikakken bayanin rayuwar ɗan ƙasa don karbar su a matsayin masu zabe.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, shugaban hukumar zabe, shugaban tarayyar Najeriya da tarayyar Najeriya, sune na 1 zuwa na 4 da ake kara.
Masu shigar da kara sun yi ikirarin cewa suna da damar shiga harkar zabe, sun kuma bukaci kotun da ta bayar da umarnin a yi musu rijistar zabe a shekarar 2023 da kuma dukkan zabuka a duk inda suke a fadin duniya kamar yadda sashe na 13, 14, 42 da 17 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 ya tanada.
Har ila yau, masu shigar da karar sun nemi kotun ta bayyana cewa har yanzu akwai isasshen lokacin da INEC za ta bi ta tanade-tanaden sashe na 13, 14 da 15 na kundin tsarin mulkin 1999.
Mai shari’a Inyang Edem Ekwo, wanda zai saurari karar, ya sanya ranar 19 ga watan Junairu, 2023, domin baiwa wadanda ake kara damar gabatar da martanin nasu.