Home Wasanni Najeriya ta gayyaci dan wasan Kano Pillars Lakosa gasar cin kofin duniya

Najeriya ta gayyaci dan wasan Kano Pillars Lakosa gasar cin kofin duniya

0
Najeriya ta gayyaci dan wasan Kano Pillars Lakosa gasar cin kofin duniya

Daga Abba Ibrahim Gwada

Kocin tawagar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr, ya fitar da sunayen ‘yan wasa 30 wadanda daga cikinsu ake saran za su wakilci kasar a Gasar Cin Kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni a kasar Rasha.

Cikin ‘yan wasan akwai tsohon dan wasan Chelsea Mikel Obi da Ahmed Musa da Odion Ighalo da Victor Moses da dai sauransu.

A cikin wadannan ‘yan wasan ne kocin Super Eagles din zai zabi ‘yan wasa 23 wadanda za a tafi kasar Rasha da su don fafatawa a gasar wadda za a fara ranar 14 ga watan Yunin bana.

A ranar 4 ga watan Yuni ne mai koyar da yan wasan zai aikewa hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) sunaye ‘yan wasa 23.

Ga sunayen yan wasan da aka gayyata da kungiyoyin da suke bugawa wasa:

Masu tsaron raga: Ikechukwu Ezenwa (Enyimba FC); Francis Uzoho (Deportivo La Coruna, Spain); Daniel Akpeyi (Chippa United, South Africa); Dele Ajiboye (Plateau United).

Yan wasan baya: Abdullahi Shehu (Bursaspor FC, Turkey); Tyronne Ebuehi (Ado Den Haag, The Netherlands); Olaoluwa Aina (Hull City, England); Elderson Echiejile (Cercle Brugge KSV, Belgium); Brian Idowu (Amkar Perm, Russia); Chidozie Awaziem (Nantes FC, France); William Ekong (Bursaspor FC, Turkey); Leon Balogun (FSV Mainz 05, Germany); Kenneth Omeruo (Kasimpasa FC, Turkey); Stephen Eze (Lokomotiv Plovdiv, Bulgaria).

Yan wasan tsakiya: Mikel John Obi (Tianjin Teda, China); Ogenyi Onazi (Trabzonspor FC, Turkey); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Oghenekaro Etebo (UD Las Palmas, Spain); John Ogu (Hapoel Be’er Sheva, Israel); Uche Agbo (Standard Liege, Belgium); Joel Obi (Torino FC, Italy); Mikel Agu (Bursaspor FC, Turkey).

Yan wasan gaba: Ahmed Musa (CSKA Moscow, Russia); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Victor Moses (Chelsea FC, England); Odion Ighalo (Changchun Yatai, China); Alex Iwobi (Arsenal FC, England); Nwankwo Simeon (Crotone FC, Italy); Junior Lokosa (Kano Pillars).