
Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewar zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben 2019 a karkashin jam’iyyar PDP nan da makonni biyu masu zuwa.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewar, za’a yi wannan gagarumin taro ne a a babban birnin tarayya Abuja.
Wazirin na Adamawa ya bayyana aniyarsa ne a ranar Asabar a babban birnin tarayya Abuja, inda ya kaddamar da yakin neman zabe na kwararo kwararo domin zaben Atiku Abubakar.
A yayin wannan kaddamarwa, a mataki na kasa da jihohi an kaddamar da mutanen a zasu jagoranci sabuwar kungiyar, Shugabanta na kasa shi ne Wabara Gerald.
Wazirin Adamawa, wanda Aliyu Bin Abbas shugaban hadaddiyar kungiyarnan ta masu rajin karewa tare da tabbatar da goyon bayan Atiku Abubakar ta AACO, shi ne ya wakilci Atiku Abubakar a wajen taron.
A cewarsa, tsohon mataimakin Shugaban kasa, ya yanke shawarar tsayawa zaben ne a sakamakon irin kiraye kirayen da yake samu daga dumbin magoya bayansa da kuma ‘yan Najeriya da suke kiran ya tsaya domin neman Shugabancin Najeriya.
“Sauran kadan na zubar da hawaye, a lokacin da yace na wakilce shi (Atiku Abubakar) yace a sauya ranar taron domin na samu na wakilce shi, ya kuma nuna gamsuwa da jin dadinsa ga irin goyon bayan da yake samu daga ‘yan Najeriya”