Home Labarai Nan da Disamba za mu kammala aikin gidajen yarin Kano, Rivers da Abuja — Gwamnati

Nan da Disamba za mu kammala aikin gidajen yarin Kano, Rivers da Abuja — Gwamnati

0
Nan da Disamba za mu kammala aikin gidajen yarin Kano, Rivers da Abuja — Gwamnati

 

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a jiya Litinin, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kammala ginin gidajen yari uku masu cin fursinoni 3,000 ko wanne nan da watan Disambar shekarar nan.

Waɗannan gidajen yarin sun haɗa da na Kano, Rivers da Abuja.

Aregbesola, ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan wani rangadin da ya kai gidan yarin da ke Karshi, Abuja, mai cin fursinoni 3,000.

Ya ce an kusa kammala wanda ke Kano yayin da aka kammala kaso 55% na aikin da ke Rivers da Abuja.

“Burina shi ne a samu guda uku na farko daga cikin ayyuka shida da za a kammala kafin wannan gwamnati ta ƙare.

“Muna da irin wannan wurin a Kano wanda ya kusa kammaluwa. Na yi imanin kafin watan Disamba, shugaban kasa ne zai ƙaddamar da shi.

“Wanda a Jihar Rivers ya kusa kaiwa irin wannan matakin. Tare da goyon bayan shugaban kasa, wadannan biyu (Rivers da Abuja) za a kammala su nan da karshen shekara,” inji shi.