
Samson Oluwamodede, wani fitaccen Fasto na darikar Evangelist a yankin Kudu-maso-Yamma, ya yi duba na malumta cewa na “habɓakar” tattalin arzikin Nijeriya, yana mai cewa nan ba da jimawa ba darajar Naira za ta dawo sosai.
Faston, wanda shi ne babban limamin Cocin Cibiyar Addu’a ta Ubangiji, PCCG, Oluwamodede, ya yi hasashen cewa ɓatagarin da ke yaƙi da ci gaban al’ummar kasar nan, da suka sa tattalin arzikin kasar ya shiga cikin mawuyacin hali nan ba da jimawa ba za su yi da na sani a shekara mai zuwa.
Malamin da ke Akure, wanda ya bayyana hakan a babban birnin jihar Ondo, ya karfafa wa ƴan Nijeriya gwiwa da su yi addu’a da gaske don neman kariya daga “masifun” a watannin da suka rage na shekara.
A cewarsa, ruhi mai tsarki, a cikin wahayi ya shaida masa cewa Naira da a yanzu ta haura Naira 700 a kan dala za ta dawo N10.
Yayin da yake jaddada cewa ba ya yin hasashen malumta na ƙarya, malamin ya ce ya taɓa yin hasashen cewa Tobi Amusan zai kawo ɗaukaka ga Najeriya.
“Yau, ni ma ina so ku yi ma maganata alama. Dala za ta fado kuma Naira za ta samu karfinta. Kamar wasan kwaikwayo, zai zama abin mamaki ga ’yan Najeriya. Na sake maimaitawa, za mu sami dala (daya) a matsayin N10 ga kudin mu.
“Kun tuna na taɓa yin hasashen malumta cewa wata budurwa za ta fito da daukakar kasar nan ta hanyar gasar wasanni kuma hasashen nawa yai daidai. Uwargida, Amusan (Tobi) ta zame mana abar alfahari a yanzu.
“Tattalin arzikinmu zai bunkasa kuma zai shafi dukkan bangarorin da za su sake farfaɗo wa,” in ji shi.