
Kanfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ce ya samar da na’urar ɗaukar hoto mai tashi a dukka yankuna shida na ƙasar nan domin bunƙasa harkar ɗaukar labarai a taruka da bukukuwa.
Da ya ke jawabi a yayin taron ƙarawa juna sani na mahukunta, Babban Manajan NAN, Buki Ponle ya ce kamfani ya ɗora ɗambar zama abin runguma ga masu ruwa da tsaki da ma wadanda su ke yin rijista da shi.
Ya ƙara da cewa matakan da kamfanin ke ɗauka na bunƙasa aiyukansa zai taimakawa abokan hulɗar sa.
Ya ƙara da cewa sabbin fasahohin da kamfanin ya kawo domin ɓangaren yanar gizo na kamfanin zai ci gaba da kawo bunƙasa wajen kawo rahotanni sahihai da kuma taimakawa aikin jarida.