Home Labarai NAPTIP ta tseratar da yara 35 da za ai safarar su zuwa nahiyar turai

NAPTIP ta tseratar da yara 35 da za ai safarar su zuwa nahiyar turai

0
NAPTIP ta tseratar da yara 35 da za ai safarar su zuwa nahiyar turai

 

Hukumar Yaƙi da Safarar Ɗan’adam, NAPTIP ta tseratar da yara 35 da za a yi safarar su zuwa nahiyar Turai a Ƙasar Nijar.
Shugaban Shiyyar Kano na hukumar, Abdullahi Babale shi ne ya baiyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a jiya Juma’a.
Ya ce an miƙa waɗanda a ka tseratar ɗin  ga jami’an Hukumar kula da Shige da Fice ta Ƙasa, inda su kuma su ka miƙa su ga Hukumar NAPTIP a bodar Kongolam da ke  Maiadua a Jihar Katsina.
Ya ce waɗanda a ka tseratar ɗin sun haɗa da maza 6 da mata 29 kuma ƴan shekaru 6 ne zuwa 42 da a ka yi safarar su da ga jihohin Ondo, Lagos, Enugu, Anambra, Oyo, Imo, Ogun, Ekiti, Edo, Osun, Kogi da Abia.
“Za a tafi da su zuwa nahiyar Turai ne ta bodar Nijar kuma mun fara bincike a kan lamarin,” in ji Babale