
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce kayen da jam’iyyar ta sha a zaben gwamnan jihar Osun a ranar 16 ga watan Yuli zai zama darasi ga jam’iyyar gabanin zaben 2023.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party, Ademola Adeleke, ya doke gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar APC, Gboyega Oyetola, a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli.
Da yake magana a wata hira da Sashen Hausa na BBC, Mista Adamu ya ce bayan shan kayen da aka yi, ya bayyana cewa akwai rikici a jam’iyyar.
Don haka Adamu ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ka ji haushin su da su zage damtse domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.