Home Siyasa Nasiru Gawuna ya ajiye muƙaminsa na Kwamishinan Noma

Nasiru Gawuna ya ajiye muƙaminsa na Kwamishinan Noma

0
Nasiru Gawuna ya ajiye muƙaminsa na Kwamishinan Noma

 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi murabus a matsayin Kwamishinan Noma na jihar.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Gawuna ya bis sahun Kwamishinoni 7 da su ka yi murabus a yau Lahadi, bayan da Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin cewa duk mai muƙami a gwamnatinsa da ya ke son tsaya wa takara a zaɓukan 2023 to ya ajiye muƙamin nasa.

A sanarwar da kakakinsa, Hassan Musa Fagge ya fitar a yammacin Lahadin nan, Gawuna ya gode wa Allah da ya bashi hikima da karsashi na riƙe Ma’aikatar Noma tsawon shekaru 7 a Gwamnatin Ganduje.

Gawuna ya ƙara da cewa a wannan shekaru bakwan, ya samu ilimi mai ɗaumbin yawa da ya buɗe ƙwaƙwalwarsa ya samu hikimar tafi da Ma’aikatar Noma, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ganduje, har ya samu nasarori da dama.

“Ina mai godiya da a ka bani damar riƙe Ma’aikatar Noma har zango biyu, a ƙarƙashin jagorancin Shugaban mu, Gwamna Ganduje, wanda har hakan ya sanya na shiga sahun Kwamishinonin Noma mafi dadewa a ƙasa baki ɗaya,”

Sai dai kuma a sanarwar, Gawuna bai nuna cewa zai tsaya takarar gwamnan Kano ba.

Amma kuma, Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an daɗe a na raɗe-raɗi cewa yana da burin tsaya wa takara domin ya gaji mai gidansa Ganduje.