Home Labarai Nazari Akan Sako ‘Yan Matan Dapchi

Nazari Akan Sako ‘Yan Matan Dapchi

0
Nazari Akan Sako ‘Yan Matan Dapchi
Daga Mahmud Isa Yola
Tun bayan  dawo da yaran makaranta da ‘yan Boko Haram suka yi awun gaba da su makwanni da suka wuce a garin Dapchi dake jihar Yobe, mutane sun yi ta bayyana fahimtan su, wasu na korafi, wasu na zargin hanun gwamnati, wasu na farincikin sako yaran.
Tambayoyi ko ta ina. Daga cikin tabayoyin jama’a akwai: “Waye ne ya sace yaran matan; Menenne aka biya kafin aka sako yaran matan; Ministan yada labarai yace karfe 3am (dare) aka sako yaran amma kuma mazauna garin sun ce da safiya ne; Yaushe ‘yan Boko Haram suka taba sakewa da jama’a da har za su yi musabiha da ‘yan gari; Yaya aka yi har ‘yan Boko Haram suka dawo da yaran matan babu jami’an tsaro da suka kama su….
“Idan kuma ‘yan Boko Haram din ba’a biya su komai ba, to menene dalilin da yasa suka sako yaran matan; idan saboda yaran musulmai ne, ai sun sha kama musulmai su ki sake su; menene dalilin sako yaran matan; Me yasa gwamnatin Nijeriya bata fito tayi bayani filla-filla game da sace yaran matan ba…”
Nasan akwai tambayoyi da yawa, kuma kowanne na bukatan amsa. Amma zan so farawa da jaddada farinciki na ga Allah da ya dawo da yaran lafiya, da kuma jinjina ga gwamnatin shugaban kasa Buhari da duk wanda ya kokarta wajen sako su. Babu wani abin farinciki game da lamarin nan fiye da dawowan su. Sannan ina so masu tambayoyi suma su yi wannan farinciki.
Kowani dan Adam yana da fahimta da Allah ya ma sa. Kuma kowa yana fadin abu ne a bisa yanda yake gani. Ina nufin fahimta fuska ce, kowa da irin ta sa. Wannan yasa komai zaka fada, kowa da yanda zai fahimce ka. Sannan kuma fahimta yana da alaka da ilimi. Ma’ana, fahimtar mutum dangane da abu ya danganta ga ilimin rayuwa da yake da shi, ko kuma sabuwa da wannan abu, wanda shime zamu iya cewa ilimin wannan abu.
A fahimta ta, lokacin da aka sace ‘yan matan Dapchi mutane ba su tada jijiyoyin wuya kamar yanda yanzu suka tayar da aka sako su ba. Wannan kuma ko dai yana nufin mutanen da suke tada jijiyoyin wuya yanzu a lokacin da aka sace  yaran matan hakan ya burge su, amma sako yaran matan ya musu zafi saboda basa so su yaba kokarin gwamnati a kai, ko kuma suna ganin cewa gwamnati bata da kokarin da zata ingiza Boko Haram ta dawo da yaran nan.
Ko ma wanne ne daga cikin fahimta biyun nan mutum ya dauka hatsari ne ga dukkan mu ‘yan Nijeriya.
 (Don in kare kai na, nayi rubutu a shafin wannan jarida a lokacin, na daura alhakin sace su akan sakacin gwamnati da gazawar jami’an tsaro. Kuna iya nema ku karanta)
Idan kace kana farinciki don an sace ‘yara karkashin gwamnatin APC, kuma kana jin zafin an sako su saboda kai a ganin ka sace yaran matan yasa gwamnatin APC ta yi kama da ta PDP, to kana da matsala a fannin fahimta. Ina nufin tushen fahimta, wato ilimi. Jahilcin ka ya rufe fahimtar ka.
Idan kuma kace kana gani gwamnatin Nijeriya bata da wani bajinta da zata iya yi har ‘yan Boko Haram su sako yaran matan nan, to kana da matsala saboda ka yanke kauna ga gwamnati. Masu nazarin fasahar dan Adam suka ce duk lokacin da mutum ya yanke kauna (hope), to basirar sa na aikata daidai a wannan abun da ya yanke kauna ya tafi. Kaga kana da matsala kenan.
A fahimta ta, babu abun farinciki da yakai  dawowar yaran matan nan cikin aminci ga iyayen su. Ina da kanne ‘yan makarantan Sakandire, bana tsammanin bayan an sace su, idan aka dawo da su zan tsaya kalubalantar gwamnati da tayi ruwa tayi tsaki (bisa dukkan alamu) akan dawo da yaran. Idan da haka ne gwamnatin da ta gabata ta yi, to da bamu dade muna jimamin sace yaran matan Chibok ba.
A fahimta ta, (ina yawan maimaita fahimta saboda muna magana ne akan fahimtar): Bai kamata mu kalubalanci gwamnati akan sako yaran matan Dapchi ba. Abunda ya kamata mu kalubanaci gwamnati akai shine sace yaran da aka yi da ranar Allah, ido na ganin ido. Aka tafi da su zuwa waje mai nisa.
Jaridar Premium Times ta ruwaito hirar da wakilin ta yayi da daya daga cikin yara matan. Yarinyar tace “Sun shigo suna harbin bindiga, suka ruda mu, sai wani yace mana mu zo ta kyauren makarantar mu same shi. Sai aka kawo manyan motoci aka saka mu a ciki. Aka yi ta dogon tafiya da mu, kafin aka tsaya, suka tambaye mu suwaye suke azumi, suka baiwa masu azumi Maltina da nama. Sai muka yi sallah kafin muka cigaba da tafiya.
“Mun cigaba har muka kai wani wuri dake da babban itace, sai muka tsaya, suka saka mu muka dafa abinci, bayan mun ci abinci sai muka cigaba da tafiya…” inji yarinyar.
Wannan yana nuna ba Aljanu ne aka yi amfani da su  wajen safaran yaran ba, mutane ne, kuma ba wai daji aka dugunzuma da su akan dawakai ba, a cikin motoci aka fita da su, kuma ana tsayawa cin abinci da sallah, duk a cikin Nijeriya, amma ace jami’an tsaro su kasa damke su. Wannan shine abun tambaya ba sako yaran matan ba.
Daga karshe, ina jinjina wa gwamnati kan rawar da ta taka wajen sako yaran matan, sannan kuma ina kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara inganta harkar tsaro a jihohin da suke fama da wannan ta’addanci, ta hanyar yalwata makaman yaki na zamani da kuma karfafa hukumar bayanan sirrin (intelligence department).
Za’a iya samun marubuci a:
+2348106792663 (text)