
Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa, NBC ta hana sanya sabuwar waƙar Ado Gwanja mai taken ‘warr’ a gidajen Radiyo da Talabijin na ƙasar .
Hakan ya zo ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da kwanan watan 6 ga watan Satumba, 2022.
Sanarwar da tace an dakatar da sanya wakar ne a radiyo da talabijin sabo da wasu kalamai da ya ke yi a cikin baitocin waƙar, waɗanda su ka saɓa da dokokin hukumar da kuma al’adar Hausawa.
Sanarwar tace waɗannan baitoci da suke cikin wakar ta Warr sun saɓawa sashe na 3, 18, 2(c) na hukumar dake kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC.
Saɓawa wannan umarni na hukumar NBC ga kafafen yaɗa labarai na rediyo da talabijin zai iya sanyawa a hukunta kafar yaɗa labaran, inji sanarwar.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa sabbin wakoki biyu da Gwanja ya fitar da su ‘warr’ da ‘chas’ na nan na shan suka duba da yadda yanayin waƙoƙin ke zama barazana ga tarbiyya.
Jaridar nan ta gano cewa Gwanja har zagi ya ke yi a cikin wasu baitukan wakar ‘warr’ ɗin, inda hakan ya saɓawa addini da al’adar mutanen Kano.
Hakan ce ma ta sanya wasu lauyoyi guda 9, su ka shigar da ƙorafi gaban Kotun Shari’ar Muslunci, wacce tuni ta baiwa ƴan sanda damar bincikar Gwanja ɗin da sauran mutane 6 bayan ƙorafin da lauyoyin su ka shigar.