Home Labarai NCAA ta dakatar da kamfanin Azman Air

NCAA ta dakatar da kamfanin Azman Air

0
NCAA ta dakatar da kamfanin Azman Air

 

Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Ƙasa, NCAA ta dakatar da kamfanin na Azman Air ne a yau Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta dakatar da Azman ne saboda rashin sabunta lasisinsa na sufurin jirgin sama, wanda a turance a ke kira da Air Operator Certificate (AOC).

Dakatarwar ta zo ne ƴan watanni bayan NCAA ta dakatar da Dana Air a kan AOC saboda abubuwan da su ka faru akai-akai, in ji jaridar Leadership.

Ya zuwa karfe 10:43 na safiyar yau Alhamis, duk zirga-zirgar jiragen saman da ke shigowa da kuma fita hanyoyin jirgin ba sa kan jadawalin, a cewar shafin yanar gizon kamfanin.

Duk da haka, an gano cewa AOC na kamfanin ya kare ne a cikin watanni 3 na farko na 2022, kuma hukumar da ke kula da su, ta hannun masu bincikenta, ta yi aiki tare da kamfanin a kan tsarin sabunta wa, amma kamfanin ya ci gaba da gaza sabunta wa.

Har ila yau, an gano cewa, kafin hukumar ta dakatar da lasisin gudanar da zirga-zirgar jiragen, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama (DATR), wani sashe a cikin NCAA, ya rubuta wasikar tunatarwa ga jami’an kamfanin na Azman Air tare da ba shi wa’adin kwanaki 30. bi ka’idojin masana’antu, amma ya kasa yin biyayya.