
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa, NCAA ta sanar da dakatar da lasisin zirga-zirgar jiragen sama na Dana Airlines (ATL) da kuma takardar shaidar yin amfani da jiragen sama (AOC) har sai baba-ta-gani.
Hukumar ta NCAA ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Musa Nuhu, Darakta Janar na hukumar ya sanyawa hannu a jiya Laraba a Legas.
An dakatar da lasisin aiki na Dana bayan da hukumar “ta gano cewa kamfanin jirgin ya gaza cika wajibcin biyan kuɗaɗe da kuma gudanar da tashi da saukar jiragensa lafiya”.
A cewar NCAA, dakatarwar ta fara aiki ne daga tsakar dare na ranar Laraba, 20 ga Yuli, 2022.
Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa: “An dakatar da shi ne bisa ga sashe na 35 (2), 3 (b), da (4) na dokar zirga-zirgar jiragen sama, 2006 da kuma sashi na 1.3.3.3 (a) (1) na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya. Dokokin Jiragen Sama, 2015.
“Shawarar ita ce sakamakon binciken kudi da tattalin arziki da hukumar ta gudanar a kan kamfanin, da kuma sakamakon binciken da aka gudanar a kan harkokin sufurin jiragen sama na kwanan nan, wanda ya nuna cewa Dana Airlines ya gaza ciks wajibcin kudi da gudanar da ayyukan jirgin lafiya.”