Home Lafiya NCDC ta aika tawogar ko-ta-kwana zuwa Jigawa, Yobe Katsina a kan cutar sanƙarau

NCDC ta aika tawogar ko-ta-kwana zuwa Jigawa, Yobe Katsina a kan cutar sanƙarau

0
NCDC ta aika tawogar ko-ta-kwana zuwa Jigawa, Yobe Katsina a kan cutar sanƙarau

Cibiyar Kula da Yaɗuwa da Daƙile Cututtuka ta Ƙasa, NCDC, ta aike da ko-ta-kwana, RET, zuwa Jigawa, Yobe da Katsina a kan cutar sanƙarau.

Dokta Pricilla Ibekwe, Shugabar Sashen Ayyuka na Musamman da Haɗin gwiwa a NCDC, ta bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja, yayin taron mako-mako na ministoci kan yin duba a kan yaƙi da cutar COVID-19 da ci gaba a fannin kiwon lafiyar ƙasar.

Ibekwe ta ce tura hukumar ta RET, ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar kan karuwar masu kamuwa da cutar sankarau da ake zargi.

Cutar ta sanƙarau ta kasance babban kalubalen kiwon lafiyar jama’a, wanda ke shafar kasashen da ke fama da cutar sankarau, ciki har da jihohi 25 da babban birnin tarayya, FCT, a Najeriya.

Ibekwe ta ce rahotannin farko na mutane 117 da ake zargi da kuma 12 da aka tabbatar sun kamu da cutar, tare da adadin waɗanda su ka mutu, CFR, na kashi 27 cikin 100 daga mako na EPI 49 2022 da EPI Week II na 2023.

“Mun kuma samar da kayayyakin aiki.

“A daya bangaren kuma, saboda kusancin jihohin Jigawa da Yobe da Katsina, mun kuma tura mambobin RRT zuwa Yobe da Katsina domin tantancewa, da inganta matakin shirye-shiryen da kuma gudanar da bincike mai zurfi na CSM don gano wadanda su ka kamu da cutar tun da wuri,” in ji ta