Home Labarai NCoS ta ƙaryata rahoton rikici a gidan yarin Kuje ta kuma tabbatar da mutuwar fursuna 1

NCoS ta ƙaryata rahoton rikici a gidan yarin Kuje ta kuma tabbatar da mutuwar fursuna 1

0
NCoS ta ƙaryata rahoton rikici a gidan yarin Kuje ta kuma tabbatar da mutuwar fursuna 1

 

 

 

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran hali ta Ƙasa, NCoS, reshen babban birnin tarayya Abuja, ta ce babu wata hayaniya a gidan kurkukun Kuje kan mutuwar wani fursuna.

Ta kuma yi watsi da wani labari da wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo suka wallafa na cewa an samu rikici daga fursunonin gidan yarin, sakamakon mutuwar wani fursuna.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Chukwuedo Humphrey ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata a Abuja.

NCoS, duk da haka, ta tabbatar da mutuwar wani fursuna a ranar 29 ga Agusta bayan doguwar jinya.

Humphrey ya ce rahoton ba gaskiya ba ne kuma ya nuna saɓanin yanayin zaman lafiya da ake samu a gidan yarin.

Lokacin da aka shigar da fursunonin a gidan yarin Kuje a shekarar 2019, ya zo da matsanancin yanayin rashin lafiya.

“Wannan shi ne abin da ya tilasta sanya shi a kan kulawar likita na musamman da gudanarwa ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatan lafiya na NCoS.

“Wannan kuma ya zo ne da wani lokaci ana kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, Gwagwalada, domin a duba lafiyarsa.

“Mun ɗauki sama da shekaru uku, mu na kula wa da lafiyarsa kyauta da sauran kulawa da tallafi don kiyaye shi saboda alhakin mu ne yin hakan,” in ji Mista Humphrey.

Ya ƙara da cewa haka a ka yi ta kula da rashin lafiyarsa har sai da ranar 27 ya ce ga garinku nan.