
Hukumar NDLEA ta kama wani dan fashi mai suna Aliyu Altine mai shekaru 19 da ake nema ruwa a jallo a kan titin Illela zuwa Sokoto a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta.
A cewar kakakin hukumar NDLEA, Mista Babafemi, an mika dan fashin jejin zuwa ga ‘yan sanda a jihar Sokoto domin ci gaba da bincike.
Hakazalika jami’an yaki da miyagun kwayoyi sun kama wasu jabun dalar miliyan 20 a yayin gudanar da aikin “Tsayarwa-da-Bincike” a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja.
Kakakin hukumar ta NDLEA ya bayyana a jiya Lahadi a Abuja cewa an gano kudaden ne na jabu a wata motar bas da ta taso daga Legas zuwa Abuja.
Ya bayyana cewa an kama direban motar mai shekaru 53, Onyebuchi Nlededin.