
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta ce kimanin miyagun ƙwayoyi miliyan 1.5 da su ka haɗa da Tramadol da Exol-5 da Diazepam ta kama a garin Onitsha na jihar Anambra da suka nufi Yauri jihar Kebbi.
Hukumar ta NDLEA ta ce ta kama magungunan ne a ranar Juma’a 14 ga watan Janairu a Jihar Edo.
A wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Femi Babafemi ya fitar a yau Lahadi,
NDLEA ta ce, a ranar Juma’a 14 ga watan Junairu 2022 jami’an tsaro a jihar Edo sun kama wata tirela da ta taho daga Onitsha zuwa Yauri a jihar Kebbi.
Binciken da aka yi wa babbar motar ya kai ga gano wasu abubuwan da suka shafi tunanin mutum da aka boye a karkashin ingantattun kayayyaki.
Ya ce magungunan da aka kama sun hada da: capsules 394,480 da Tramadol 3,000 masu nauyin kilogiram 83.707 da Exol-5 647,500 masu nauyin 203.315kg sai Diazepam 12,500 masu nauyin 2.05kg da Bromazepam 1,500 masu nauyin 0.45kg da maganin ruwa na Syrup tushen Codeine kwalabe 999 masu nauyin 134.865kg da kuma Allurar Pentazocine 4,000 ampoules masu nauyin 16.64kg.
An kama direban motar Bashir Lawali mai shekaru 30 tare da Abubakar Sani mai shekaru 30 da kuma Ali Abubakar mai shekaru 19, yayin da aka kwace kayayyakin tare da holin su a Kano, da hannun wani Sa’idu Yahya mai shekaru 31.