
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA, ta ce ta kama kilo-giram ɗaya na hodar ibilis da kuma kilo-giram 511.3 na tabar wiwi a ranar Laraba a Jihar Kaduna, inji Kwamandan Hukumar na jihar, Umar Adoro.
Da ya ke taron nema labarai a jiya Asabar, Adoro ya ce a tashar mota ta Mando ne jami’ansa su ka kama kilo ɗaya na hodar ibilis su ka kuma cafke mutane 2 a ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa, a ranar 11 ga watan Afrilu ne kuma hukumar ta kwace yanar wiwi mai nauyin kilo-giram 441 da ga wani mai laifi wanda tuni ya shiga hannu.
Ya ci gaba da cewa, ko a ranar Laraba ma sun kama kilo 12.1 na wiwi kuma sun kama mai ita, inda ya ƙara da cewa sun kama miyagun kwayoyi da masu su a kan Abuja zuwa Kaduna.
Adoro ya ce a ranar 17 ga Afrilu jami’an NDLEA sun kama kilo 3 na wiwi kuma sun kama mai ita a kan titin Makarfi a unguwar Rigasa, cikin birnin Kaduna.
Sannan ya ce a ranar 21 ga Afrilu ma jami’an hukumar sun kama kilo 10.y na tabar wiwi da kuma masu ita a kauyen Kargi na Karamar Hukumar Kubau a Kaduna, da dai sauran miyagun ƙwayoyi da hukumar ta kakkama a jihar a kwanan nan.