
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kama wani fitaccen mai haɗa wani abin sha da ke taɓa ƙwaƙwalwa, wanda aka fi sani da Akurkura a Kano.
Jami’an NDLEA ɗin sun cafke Qasim Ademola, inda su ka damƙe kwalabe 26, 600 na kayan mayen da aka tanada domin rabawa a fadin jihohin Arewa.
An kama kayan ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba a kan hanyar Zaria zuwa Kano, Gadar Tamburawa.
A nan ne kuma a ka cafke mai haɗa sinadarin, mai shekaru 39 ɗan karamar hukumar Akinyele, jihar Oyo da uku daga cikin masu rarraba shi a wani samame da aka yi.
Shugaban Hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya yabawa hafsoshi da jami’an rundunar a Kano bisa yadda suke ƙwazo da jajircewa wajen gudanar da ayyukan su
Ya kuma umarce su da sauran su a fadin kasar da su ci gaba da mai da hankali yayin da suke sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.