
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA ta sanya a nemo mata shararren ɗan sandan nan, Abba Kyari ruwa a jallo a kan zargin miyagun kwayoyi mai nauyin kilogiram 25.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ne ya baiyana hakan a taron manema labarai a Abuja a yau Litinin.
NDLEA ta ce binciken ta yaya nuna nata cewa Kyari mamba ne nan wata ƙungiyar masu kasuwancin miyagun kwayoyi ta duniya.
A tuna cewa Kyari, wanda ya ke matsayin Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda ne, a yanzu haka an dakatar da shi da ga aiki sakamakon zargin alaƙa da sanannen ɗan famfarar nan na duniya, Ramon Abbas, wanda a ka fi sani da Hushpuppi.
Ƙarin bayani na nan gaba…