
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta gayyaci wani shugaban karamar hukuma a Jihar Neja bisa muku zargin sa da karfafa wa matasa gwiwa kan shaye-shayen miyagun kwayoyi.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, an yi zargin cewa shugaban karamar hukumar ya na gaya wa gungun matasa da su rika amfani da harabar sakatariyar karamar hukumar a duk lokacin da su ke son shan tabar wiwi.
Haruna Kwetishe, kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Minna, a yau Alhamis cewa hukumar ta mika goron gayyata ga shugaban.
“Mun rubuta wa shugaban karamar hukumar wasikar gayyata kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta.
“Wani ya yi zargin cewa shi ne ya shawarci matasan da su yi amfani da sakatariyar karamar hukumar domin shan tabar wiwi, wanda aka fi sani da marijuana, duk sanda su ke buƙata ne.”
Mista Kwetishe ya ce hukumar ba za ta bari kowa ya rage kokarin da hukumar ke yi na yaki da miyagun kwayoyi da muggan kwayoyi ba.