
Daga Hassan Y.A. Malik
Wani tsoho mai shekaru 64 ya shiga hannun jami’an hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi NDLEA a karamar hukumar Egor da ke jahar Edo, bayan da aka samu buhuhunan tabar wiwi jibge a cikin silin din gidan shi.
Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa da kwamandan hukumar, Buba Wakawa ya fitar a Benin, babban birnin jahar.
Tsohon mai suna Daniel Idemudia ya tabbatar da cewa ya na sane da ajiyar buhuhunan, amma ba mallakin sa ba ne.
Jaridar Vanguard ta rahoto Idemudia ya na cewa wani abokin shi ne ya kawo masa ajiya, kuma ya yi masa alkawarin biyan shi da zaran ya kammala sayar da su.
Banda wadannan buhuhunan, hukumar ta kuma samu buhuhuna 245 a wani dakin ajiye kaya a karamar hukumar Ovia South da ke jahar.
Za a gurfanar da Idemudia a kotu da zaran an kammala bincike akan shi, kamar yadda hukumar ta bayyana.