Home Wasanni Neymar ya koma filin domin cigaba da karbar horo

Neymar ya koma filin domin cigaba da karbar horo

0
Neymar ya koma filin domin cigaba da karbar horo

Daga Abba Ibrahim Gwale

Dan wasan kasar Brazil da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta PSG ta Faransa, Neymar Junior ya koma filin daukar horo ka’in da na’in bayan shafe kusan watanni uku yana jinya sakamakon karayar da ya samu a kafarsa.

Neymar dan wasa mafi tsada a duniya, rabon shi da filin kwallo tun karshen watan Fabarairu, ko da yake dai a makwanni biyu da suka gabata bayan fitowarsa daga asibiti an fara ganinsa a filin kwallo amma yana dogara sanda.

A cewar mai horar da tawagar kwallon kafar Fabio Mahseredjian ana samun gagarumin ci gaba a lafiyar dan wasan mai shekaru 26 wanda su ke kyautata zaton zai yi rawar gani a gasar cin kofin duniya ta bana da za ta gudana a Rasha.

Neymar din dai na cikin jerin ‘yan wasan da za su wakilci kasar Brazil a Rasha nan da kwanaki 22 masu zuwa, kuma ana fatan nan da ‘yan kwanaki kalilan zai zanzare ta hanyar fara karvar atisaye kamar kowa.

A kwanakin baya dai anyi zaton dan wasan bazai buga gasar ta cin kofin duniya ba abinda yasaka tsoro a zuciyar hukumar kwallon kafar Brazil.

Tuni dai dan wasan shima yace ya shirya kuma zai buga gasar cikin kwarjini da walwala kuma yayi alkawarin zai farantawa magoya bayan kasar rai a Rasha.