
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar, dan asalin kasar Brazil yana daukar albashin sama da naira miliyan arba’in da uku a kullum, kamar yadda bincike ya bayyana.
Neymar bai buga wa Paris St. Germain gasar cin kofin Faransa wato Ligue 1 a karawar da ta tashi babu ci da Montpellier a ranar Asabar, sakamakon jinya da yake yi.
Dan wasan ya koma PSG da taka-leda kan fam miliyan 200 daga Barcelona a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya a fagen tamaula.
Sai dai ana rade-radin cewar dan wasan na tawagar Brazil ya na karbar fam 88,552 a kowacce rana, kimanin fam miliyan 2,718,126 a duk wata.
Mujallar Der Spiegel ce ta fitar da wannan rahoton inda ta kara da cewar Neymay yana karbar fam 3,542 a duk sa’a daya kamar yadda Marca ta wallafa.