
Daga Mansur Ahmed.
Kimanin watanni biyu da suka gabata d’aya daga cikin mutanen da basa kunyar yiwa talakawa Najeriya k’arya Ministan harkokin sufuri, Hadi Sirika ya kaddamar da kamfanin sufurin jirage da baki, mai suna ‘NIGERIA AIR’, da yammacin jiya gwamnatin tarayya ta bada sanarwar dakatar da shirin cewar sai lokacin da jaki yayi k’aho.
Hadi Sirika shine yayi kid’an kuma shine yayi rawar a lokacin da ake wani bikin nuna jirage na duniya inda ya wakilci kasar nan. Shine ya sake tabbatar da dakatarwar jim kadan bayan zaman majalisar zartaswa ta kasa a fadar Shugaban Kasa da ya gudana a jiya Labara.
Ga yadda yayi jawabin a harshen turanci a shafinsa na wannan kafar. “Ina mai bakin cikin shaida muku cewa Majalisar zartaswa ta taayya ta d’auki wani mataki na dakatar da shirin kafa Kamfanin Jiragen Sama a halin yanzu. Amma kuma dukkan yarjejeniyar da aka kulla ta na nan ba a yanke ba. Mu na godiya ga jama’a da ke goyon bayan mu a kowane lokaci.”
Dama kuma tun lokacin da aka rada wa jirgin suna ‘Nigeria Air’, muka soki shirin cewar shafcin gizo ne kawai, k’arya, yaudara, ci da mali irin na yan gwamnatin APC wadda girma baya hana su fad’ar k’arya a kowanne lokaci domin daman akan haka aka gina jam’iyyar da gwamnatin. A lokacin da suka k’addamar da shirin mun ce karya ce kawai da kuma yaudara saboda kakar zab’en 2019 ta k’arato, sannan aka bijiro da batun kafa jiragin.
A rubutun da Kwamared Baban Shareek Gumel da Maryam Shetty tayi nace musu da wannan zancen da k’aryar gizo duk sunansu d’aya, domin idan da gaskiya ne kamata ya yi gwamnatin tarayya ta yi koyi da abin da gwamnatocin baya suka yi, wajen sayowa tare da wadatar da k’asar nan da motocin sufuri domin samun sassaucin zirga-zirga a farashi mai rahusa ga talakawa.