
Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna kwarin gwiwa cewa ƴan Nijeriya za su canja yanayin mulkin kama-karya da APC ke yi a 2027.
Kwankwaso ya fadi hakan ne a yayin da ya ke karɓar mabiya jam’iyyar APC 977 na Ƙaramar Hukumar Dala da su ka bar jam’iyyar zuwa NNPP a Kano a yau Alhamis a gidan sa da ke Miller Road.
A cewar Kwankwaso, gwamnatin APC ta gaza gurin cika alkawuran da ta daukar wa ƴan Nijeriya, inda ya yi kira ga ƴan ƙasa da su yi ƙoƙari su canja gwamnatin a 2017.
“Talauci, yunwa, rashin tsaro da rashin aikin yi sai ƙaruwa su ke. Magidanta ba sa samu su ciyar da iyalan su.
“Wannan lokaci ne da ƴan Arewa da ma Nijeriya baki daya za su tashi tsaye su kawo canji da kan su.
“Su na ganin ba za a iya canja su ba saboda su na da tsaro da hukumar zabe, to idan guguwar canjin ta bisa su da kan su za su yi gudun famfalaƙi,” in ji Kwankwaso