Home Wasanni Ƴan Nijeriya na kira da a naɗa Abdu Maikaba a matsayin sabon kocin Super Eagles

Ƴan Nijeriya na kira da a naɗa Abdu Maikaba a matsayin sabon kocin Super Eagles

0
Ƴan Nijeriya na kira da a naɗa Abdu Maikaba a matsayin sabon kocin Super Eagles

 

Wasu ƴan Nijeriya sun fara kiraye-kiraye da a naɗa Abdu Maikaba, kocin Enugu Rangers a matsayin sabon kocin Super Eagles.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya Alhamis ne dai Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa, NFF, ta sallami Augustine Eguavoen da ga kocin tawogar ƙwallon ƙafar ƙasar, Super Eagles.

Sallamar ta Eguavoen ta zo ne bayan da Super Eagles ɗin ta gaza kai wa ga Gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar a 2022, bayan da ta yi 1-1 da Ghana a Abuja a ranar Talata.

Bayan sallamar Eguavoen ɗin ne, sai wasu ƴan ƙasar, musamman masu ruwa da tsaki, ke kiraye-kirayen a naɗa Maikaba ya maye gurbin Eguavoen duba da irin ƙwazonsa a fannin horaswa ta ƙwallon ƙafa.

Wani ɗan jarida mai labarin wasanni da ke zaune a Jihar Kaduna, Mohammed Mohammed, ya wallafa a shafinsa na facebook cewa a gwada Maikaba a matsayin kocin Super Eagles.

“Ya kamata a gwada Abdu Maikaba a matsayin sabon kocin Super Eagles,” Mohammed ya wallafa da turanci.

Daily Nigerian Hausa ta gano cewa bayan Mohammed ya wallafa saƙon a facebook, yawancin waɗanda su ka yi masa sharhi a ƙarƙashin saƙon sun nuna goyon bayan hakan.

Wannan jaridar ta biyo cewa Maikaba, wanda ya shafe sama da shekaru goma ya na horaswa a manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar gasar Premier ta Ƙasa, NPL, ya lashe gasar ta kakar 2019-2020 a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Plateau United da ke garin Jos.

Maikaba ya horasa da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama da su ka haɗa da Akwa United, Wiki Tourists, Plateau United, Rangers International da sauran su.

Sannan kuma ya yi mataimakin mai horasa a Kano Pillars da kuma tawogar ƙwallon ƙafar Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 20.