
Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar inganta samar da wutar lantarki a cikin gida ta hanyar yanke yawan wutar da take sayar wa da ƙasashen Nijer, Togo da Jamhuriyar Benin.
Hukumar kula da hasken wutar lantarki ta Najeriya, NERC, ta umurci wani sashe na kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya, wato ‘System Operator (SO)’, da ya rage wutar lantarki daga kasashen uku zuwa kashi shida cikin dari.
Umurnin na NERC, wanda aka buga ranar Juma’a, mai dauke da kwanan wata 29 ga Afrilu, 2024, kuma ya fara aiki daga ranar 1 ga Mayu, 2024, Shugaban Hukumar, Sanusi Garba, da Mataimakin Shugaban, Musiliu Oseni ne suka sanya hannu tare.
Umurnin, wanda aka zayyana a cikin sanarwar zai ɗauki tsawon watanni shida kawai, amma akwai damar samun canje-canje akan haka.
A cewar takardar, sayar da wutar lantarki ga makwabtan Najeriya bai kamata ya wuce kashi shida cikin dari na adadin wutar lantarki a kowane lokaci ba.
Hukumar ta nuna damuwa yadda sayar wa da kashen wutar lantarki ke hana kwastomomi a Nijeriya samun isashshiyar wuta.