Home Labarai Ƴan Nijeriya sun daina kwarmata masu satar kuɗin gwamnati, in ji EFCC

Ƴan Nijeriya sun daina kwarmata masu satar kuɗin gwamnati, in ji EFCC

0
Ƴan Nijeriya sun daina kwarmata masu satar kuɗin gwamnati, in ji EFCC

 

 

 

 

Hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ‘yan Najeriya sun sare da kwarmata bayanai kan wasu satar kudin gwamnati Tarayyar, duk da babban kudin lada da ke tattare da yin hakan.

Shugaban hukumar ta EFCC, Abdullahi Bawa, ya shaida hakan ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Kwara, wato Ilorin.

Shugaban ya ce akwai bukatar sake jan hankalin mutane da ankarar da su muhimmanci yin haka a kokarin kwato kudaden sata da sake gina tattalin arzikin kasa.

Sai dai hukumar ba ta yi karin haske ko shaida dalilan da suka sa ‘yan Najeriya suka sare da bada bayanan ba.

Tun a shekara ta 2016 gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin kwarmata bayanai da zummar bai wa ma’aikata da ɗaiɗaikun mutane damar fallasa ayyukan cin hanci da rashawa, ita kuma gwamnati ta saka musu da kuɗin lada.

A cewar Ministar Kuɗi ta lokacin, babbar hikimar ɓullo da shirin ita ce taimaka wa yaƙi da rashawa ta hanyar yawaita bankaɗo laifukan da kuma bai wa masu bankaɗowar lada.

Hakazalika a shekara ta 2021, EFCC, ta kaddamar da wata manhaja da za ta ba ‘yan kasar damar daukar hotunan abubuwa ko wuraren da ake aikata laifuka.

Da yake magana da BBC Hausa, Abdulrasheed Bawa ya ce yunƙurin nasu yana cikin shirin nan na kwarmata bayanai da ake Whistle Blower a Ingilishi.

“Duk wanda yake so ya kwarmata mata bayanai don ya samu wani abu zai iya yin hakan a ciki kuma ya bayyana cewa ya yi hakan ne a matsayinsa na mai kwarmata bayanai,” a cewarsa.