Home Cinikayya Nijeriya za ta zama babbar mai kai wa Turai iskar gas — Minister

Nijeriya za ta zama babbar mai kai wa Turai iskar gas — Minister

0
Nijeriya za ta zama babbar mai kai wa Turai iskar gas — Minister

 

 

Karamin Ministan Albarkatun Man fetur, Timipre Sylva, ya ce Nijeriya na shirin zama babbar mai safarar iskar gas ga Nahiyar Turai, sakamakon matsalar makamashin da ake fama da ita a duniya, wanda yaƙin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya haifar.

Sylva ya shaida hakan ne a jiya Talata yayin wani zagayen tattauna wa a yayin babban taron Gastech karo na 50 da ke gudana a birnin Milan, Italiya.

Ministan ya ci gaba da cewa, a halin yanzu, tallafin da ake samu na bunkasa iskar gas ya kasance nasara ga Turai da Afirka.

Ya ce: “A yau muna ganin yadda iskar gas ta zama ƴar sarki kuma kowace ƙasa za ta bukaci a kalla wata hanya ta safarar sa.

“Don haka, muna sanya kanmu mu zama madadin masu siyarwa ga Turai. Mun riga mun yi aiki tare da Algeria don gina bututun iskar gas na Trans-Sahara wanda zai dauki iskar gas din mu har zuwa Turai.

“Har ila yau, muna da haɗin gwiwa tare da Maroko don faɗaɗa bututun iskar gas na Afirka ta Yamma zuwa Maroko da tsallaka tekun Bahar Rum zuwa Turai.

“Mun yi imanin cewa Turai na buƙatar wannan iskar gas kuma hakan nasara ce ga dukkanmu kuma yana da amfani a rage waɗannan saka hannun jari na nuna wariya da bankunan su ke yi.”